QUNGIYAR HISBA TA KAMA MURJA KUNYA YAR TIK TOK

 Rundunar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama shahararriyar Æ´ar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya da laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waÉ—anda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.


Makwanni biyu da suka gabata, Hisbah ta Æ™addamar da farautar wasu Æ´an Tiktok guda shida waÉ—anda suka ce suna saÉ“a wa ka’idojin musulunci a kullum wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Kakakin Hisbah Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa an kama Murja Ibrahim Kunya da sanyin safiyar Talata, tare da saurayinta.

"Jami'anmu sun kama ta ne da karfe 1:00 na rana a gidanta tare da saurayinta, wanda shi ma yana tare da mu."

“A baya dai, makwabtanta sun kawo mana korafi game da halinta. A yanzu haka muna kan bincike kafin daukar mataki na gaba,” inji shi.

Ana zargin Murja da yin amfani da kalaman ɓatanci da rashin kunya a cikin bidiyonta, wanda dubban mutane ke kallo.

Ba ta ce uffan ba kan wannan zargi, amma an gan ta a wani faifan bidiyo da ba a tantance ba yana yawo a shafukan sada zumunta tun bayan kama ta.

A bidiyon, an jiyo ta tana cewa ba ta saci komai ba, kuma ta gode wa Allah a kan hakan.

Kano dai na da mafi yawan al'ummar Musulmi kuma tsarin shari'a na Musulunci yana aiki tare da tsarin doka a jihar.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post