GWAMNATIN JAHAR BAUCHI TA DAGA TAWAGA MAI KARFI DON RAKIYAR DAN ASALIN JAHAR BAUCHI IBRAHIM MUHAMMAD NASIR WANDA ZAI WAKILCI NIGERIA A MUSABAKAN SARKI ABDUL-AZIZ NA KASAR SAUDIYYA
Kwamishinan Kula Da Harkokin Addinai Hon Yakubu Ibrahim Hamza Ya Bayyana Wa Manema Labarai Cewa Alhamdulillahi Dukkanin Shirye-Shirye Ya Gabata Domin Gwamna Ya Daga Tawaga Mai Karfi Daga Kwamitin Musabaka, Da Zasu Raka Dantakaran Musabakan Dan Asalin Jahar Bauchi Ibrahim Muhammad Nasir Wanda Yafito Daga Shira LGA, Wanda Shine Zai Wakilci Kasar Nigeria A Kasar Saudiyya, Za'a Fara Na Tafiyan Dan Takaran Mu Wato Gwarzon Shekara Wanda Shi Zai Wakilci Kasar Nigeria A Kasar Saudiyya. Wanda Za'a Ranan 09-08-2024
Hon Yakubu Yace Tunda Gwarzon Yaci Musabakan Na National A Jahar Yobe Su Jami'ar Dan Fodiyo Dake Sokoto Sune Suke Sanar Da Jahar Bauchi Halin Da Ake Ciki Akan Musabakan Na Kasa Da Kasa Don Sanin Lokacin Tafiya, Tuni Yanzu Haka Tawagan Suntafi Suna Kasar Saudiyya Don Raka Dalibi
Yace Mun Gayyaci Malamai Da Sokoto, Da Wasu Jaha Da Alkalan Mu Na Jahar Bauchi Aka Zaunar Dashi Don Horar Da Dalibin, Muna Da Yakinin Ya Samu Bita Mai Kyau In ALLAH Ya Yarda Zamu Dawo Da Nasara Tare Da Farin Ciki.
Hon Yakubu Yace Tuni Mai Girma Gwamna Ya Cika Alkawari Dayayi Na Samar Da Gurbin Karatu A Kasar Waje, Wa Dalibai da Suka Zama Zakaru A Gasar Ta Kasa. Su Uku
1. Ibrahim Muhammad Nasir Karamar Hukumar Shira
2. Amar Muhammad Mansur Karamar Hukumar Bauchi.
3. Aishatu Ahmad Aliyu Karamar Hukumar Bogoro
Dukkanin Su Sunsamu Karatun MEDICAL DOCTOR A [ SHARDAN UNIVERSITY, INDIA ]
Shi Kuma Yaro Daya Wanda Bai Gama Secondary School Ba Sai Bana Yazana Jarabawa Na SSCE NECO DA WAEC, Wanda Shima Mai Girma Gwamna Yace Idan Yayi Jarabawa Tayi Kyau To A Nema Masa Makaranta A Kasasen Larabawa Don Shima Yayi Karatu.
Hon Yakubu Yace Mai Girma Gwamna Sen Bala Kauran Bauchi Ya Biya Dukkanin Kutin Karatun Su Na Shekara Hudu (4) Dakuma Kudin Abincin Su, Kudin Wurin Kwana Kudin Transport Dinsu, Yace Idankaga Anbasu Wani Abu To Sai Dai Ticket Dinsu Na Jirgin Domin Sun Gama Sai Dawowa.
Dagakarshe Yayi Addu'a ALLAH Yasa Ayi Nasara, Yana Rokon 'Yan Uwa Da A Tayamu Da Addu'a ALLAH Yasa Ayi Nasara Amin. Yakuma Saka Wa Mai Girma Gwamna da Alkhairi Domin Yayi Duk Abinda Ya Kamata Akan Hakan Musabaka. Tun Daga Matakin Kananan Hukumomi Har Zuwa Matakin Kasa Da Kasa.
05-08-2024

Gaskiya Masha Allah
ReplyDelete