ASHE MUTUWA DAGASKE NE

 Wato bansan haka mutuwa take ba saida naga wani hatsari ya faru a wani gari.

Ina kan hanya ta zuwa kauye ziyara can kawai muna tafiya bisa sawu sai ga wata mota ta fito aguje ta ɓarin yamma. Kai daganin wannan motar kasan birki ya kwace a motar. ba kawai sai mota ta iyo bangaren da muke tafiya ba.



Daga nanne fa nace wa wanda muke tare dasu maza mugudu a nan, na daka tsalle na fada gefen rami da zuwan mota kawai tayi awun gaba da mutum uku daya daga cikin su ya karye a cinya biyu kuwa sun mutu har lahira babu wani alamar motsi ajikin su.

Buguwar tayi musu yawa ajikinsu sosai 

Bayanda zanyi haka na tattara su wuri guda muka nemi taimakon al'umma ta hanyar tare motoci don kawo mana dauki. 

Karshen labari na daya kenan mutara gaba don jin yanda yan uwan wannan wanda suka rasu mai zai ɓullo.

1 Comments

  1. Gaskiya wannan labari akwai daukar hankali zanso naji karshensa

    ReplyDelete
Post a Comment
Previous Post Next Post